✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya raba wa iyalai 100,000 tallafi a Monguno

Sun samu tallafin tsabar kudi miliyan N325 da kayan abinci

Gwaman Borno, Babagana Zulum ya raba wa magidanta dubu dari tallafin tsabar kudi Naira miliyan 325 da kuma kayan masarufi a garin Monguno.

Zulum da kansa ya jagoranci rabon kudaden da sauran kayan tallafin ga iyalan 100,000 din da ke zaman gudun hijira a Monguno sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram.

Masu gudun hirar da aka yi wa sansani a garin Monguno sun fido ne daga Kananan Hukumomin Jihar da suka hada da Kukawa, Nganzi, Marte da Guzamala.

Kayan da aka raba sun hada da hatsi, sukari da atamfofi da aka raba wa magidanta 65,0000 da kuma mata 35,000.

An ba wa kowane magaidan buhu uku na shikafa masara da wake, matan kuma kowacce aka ba ta turmin atamfa da kudi N5,000.

A lokacin ziyarar, Zulum ya ba da filin da za a gina Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Tarayya a garin Monguno wanda Gwamnatin Tarayya ta sahale a baya-bayan nan.