✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya nada Dlakwa mukaddashin shugaban Jami’ar Jihar Borno

Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya amince da nadin Farfesa Haruna Dantoro Dlakwa a matsayin shugaban riko na Jami’ar Jihar Borno

Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya amince da nadin Farfesa Haruna Dantoro Dlakwa a matsayin shugaban riko na Jami’ar Jihar Borno da ke Maiduguri.

Nadin Dlakwa na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga sakataren gwamnatin jihar Borno, Bukar Tijjani, a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce amincewar Zulum ya biyo bayan shawarar da majalisar gudanarwar jami’ar ta bayar ne, bayan taronta na 10 da aka gudanar a ranar 15 ga Afrilu, 2024.

Kafin nadin nasa, Farfesa Dlakwa shi ne mataimakin shugaban jami’ar a bangaren ilimi.

Gwamna Zulum ya taya shi murna tare da fatan alheri zuwa lokacin da za a nada shguaban jami’ar.