✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Emefiele Ya Kashe N18.9bn Kan Buga Sabbin N684.5m —EFCC

EFCC na tuhumar tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, da kashe Naira biliyan 18.96 wurin buga sabbin takardu Naira miliyan 684

Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) ta zargi tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele,  da kashe Naira Biliyan 18.96 wajen buga Naira Miliyan 684,590,000.

Duk da cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da canza fasalin takardun Naira 200, 500 da kuma 1,000 karkashin jagorancin Emefiele, aikin ya janyowa tsohon gwamnan babban bankin ce-ce-ku-ce.

A waɗansu sabbin tuhume-tuhume hudu da EFCC ta shigar a gaban wata babbar kotun tarayya  a Abuja, ta zargi  Emefiele da taka doka da nufin cutar da jama’a a lokacin da yake aiwatar da aikin sauya takardun Naira.

Ana sa ran za a gurfanar da Emefiele a gaban babbar kotu ranar 30 ga Afrilu, 2024 kan zarge-zargen.

Ana zargin Emefiele da bijire wa doka, yin gaban kansa, wahalar da jama’a, jawo musu bacin rai da kuma cirar karin Naira biliyan 124.9 daga asusun gwamnati ba tare da amincewar majalisar tarayya ba.”