Shahararren dan kwallon Faransa da yanzu haka yake koyar da kulob din matasa na Real Madrid a Sfen Zinedine Zidane ya bayyana sunayen ’yan kwallo uku da suka fi burge shi a duk fadin duniya.
Zidane ya ce baya ga Cristiano Ronaldo dan kwallon Real Madrid na Sifen da Lionel Messi na FC Barcelona da ke Sifen na ukunsu da ya fi burge shi, shi ne Eden Hazard, dan kwallon Chelsea da ke Ingila.
Ya ce “baya ga Ronaldo da Messi, dan kwallon da na fi sha’awa shi ne Hazard musamman a lokacin da yake murza leda”.
Hazard dai ana kyautata zaton zai canza sheka daga kulob din Chelsea zuwa na Real Madrid a karshen kakar wasa ta bana ne bayan ya kasa tabuka abin a-zo-a-gani a kakar wasa ta bana.
A bara, dan kwallon ne ya lashe gwarzon dan kwallon Ingila (PFA). Sai dai a bana dan kwallon ya samu koma baya ne bayan ya zura kwallo daya kacal daga cikin wasanni 12 da ya yi wa kulob din Chelsea kawo yanzu.
Zidane ya ce yana da yakini Hazard dan kimanin 24 kuma haifaffen Beljiyam zai cigaba da haskakawa kafin a kammala kakar wasa ta bana.
Ya ce “ina da burin na ga Hazard ya koma kulob din Madrid don ya cigaba da nuna bajinta”.
Zidane ya bayyana ’yan kwallo uku da suka fi burge shi
Shahararren dan kwallon Faransa da yanzu haka yake koyar da kulob din matasa na Real Madrid a Sfen Zinedine Zidane ya bayyana sunayen ’yan kwallo…