✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ZazzabinLassa ya kashe mutum 41

Daga farkon samun labarin bullar zazzabin Lassa zuwa farkon wannan mako annobar ta hallaka akalla mutum 41 a sassan Najeriya. Hukumar Yaki da Yaduwar Cututtuka…

Daga farkon samun labarin bullar zazzabin Lassa zuwa farkon wannan mako annobar ta hallaka akalla mutum 41 a sassan Najeriya.

Hukumar Yaki da Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ce ta sanar da haka a ranar shekaranjiya Laraba, inda ta ce daga 1 zuwa 26 ga Janairu an tabbatar da cutar a kan mutum 258  da suka hada ma’aikatan lafiya  biyar a  jihohi 19 na kasar nan

Ita da cutar Lassa tana kama da ta Ebola, kuma tana barna kamar ta Ebola.

A bara ma an samu bullar cutar, inda ta hallaka mutum 170.

Hukumar ta ce duk da cewa an samu mace-macen mutane, amma idan aka kwatanta da bara abin da sauki.

Cutar Lassa ta samo asali ne daga garin Lassa da ke Jihar Borno, kuma an fara samun bullar cutar ce a 1969.

A wani bangaren kuma, cutar Conorobirus (kurona bairus) da ta bayyana a kasar China ta jefa dar-dar a zukatan mutanen Najeriya, musamman ganin yadda take hallaka mutane a kasar China da kuma yadda ta fara yaduwa zuwa wasu kasashen duniya.

Mutane sun shiga tsoro ne ganin cewa ’yan kasar China mazauna Najeriya da suka tafi hutu za su fara dawowa kasar nan.

Wannan ya sa Gwamnatin Tarayya umarci ’yan Najeriya da suke da niyyar tafiya China su dakata, sai dai idan tafiyar ta zama dole

Haka a Abuja, Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin rufe katafaren shagon nan na Panda, mallakar mutanen China da ke yankin Jabi a Abuja bisa zargin suna shigo da abincin da ake tsammanin zai iya yada cutar.

A nata bangaren kuma, Gwamnatin Jihar Legas ta ce za ta kebe mutanen China a waje daya idan suka dawo domin kiyayewa.

Gwamnatin ta ce ta dauki wannan mataki ne ta hanyar samun yarjejeniya da Ofishin Jakadancin China domin kiyaye yaduwar cutar a Najeriya.