Cibiyar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa (NCDC), ta sanar da mutum 1,154 da suka kamu da cutar zazzaɓin Lassa a Najeriya a 2024, yayin da mutum 190 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.
Shugaban Hukumar, Dokra Jide Idris ne, ya bayyana haka a Abuja, inda ya ce jihohin Ondo, Edo, Bauchi, Taraba, Benuwe da Ebonyi ne suka fi yawan adadin masu fama da cutar.
- Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa
- Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta
Adadin nasu ya wakilci aƙalla kusan kashi 90 cikin 100 na dukkanin masu cutar.
Ya kuma ce ƙananan hukumomi 10, irin su Owo, Esan ta Yamma, da Jalingo, ne suke da kashi 59 cikin 100 na adadin masu cutar.
Dokta Idris, ya gargaɗi ‘yan kasa kan ƙaruwar cutar da mutuwa a baya-bayan nan, inda ya ce hakan ya nuna yawaitar yaɗuwar cutar.
Ana kamuwa da zazzaɓin Lassa ne, ta hanyar cin abinci ko amfani da kayan gida da suka gurɓata da fitsari, kashi, ko yawun ɓerayen da ke ɗauke da cutar.
Har ila yau, cutar na yaɗuwa a tsakanin mutane ta hanyar haɗuwar jini ko sauran ruwan jikin wanda ke ɗauke da cutar.
Hukumar NCDC ta kafa cibiyar bayar da agajin gaggawa da ke raba magani a jihohin da cutar ta fi ƙamari.
Hakazalika, hukumar ta ƙara yawan ɗakin gwajin cutar zuwa 13 tare da yin ƙoƙari wajen rage yawan masu kamuwa da mutuwa sakamakon cutar a faɗin ƙasar.
Zazzabin Lassa dai cuta ce da ake samu sakamakon ƙwayar cutar Lassa, wadda ake samu a jikin ɓeraye a nahiyar Afirka.