Hukumar Yaƙi Da Cututtuka Masu Yaɗuwa a Nijeriya, NCDC ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar sanƙarau a Nijeriya ya kai 151.
Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna ƙaruwar waɗanda suka kamu da cutar daga 74 zuwa 156 a jihohin ƙasar 23.
- Sojoji biyu da gomman ’yan ta’adda sun rasu a artabu a Borno
- Zanga-zangar da za mu yi babu gudu babu ja da baya — Take It Back
Jihohin da aka fi samun yawan mace-macen sun haɗa da Kebbi, da Sakkwato da Katsina da Jigawa da Yobe da Bauchi da Gombe da Borno da Kano da Adamawa da kuma Oyo.
NCDC ta ce ta tabbatar da kamuwar wasu mutum 126 daga cikin mutum 1,858 da aka yi zargin suna dauke da cutar a jihohin ƙasar 23.
Wani rahoto da NCDC ta fitar a ranar Lahadi, ta ce jihohin Jigawa, Yobe, Gombe, Katsina, Adamawa, Kebbi da kuma Sakkwato su ne sahun gaba na masu fama da cutar a bayan nan.
Cutar Sanƙarau dai cuta ce da aka fi ɗauka galibi a lokacin zafi.
Wasu mutanen na iya yaɗa cutar ba tare da sun san suna ɗauke da ita ba, akasarin mutanen da ke ɗauke da ita ba su sani ba.