✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar sanƙarau ta yi ajalin mutum 3 a Gombe

Kwamishinan ya gargaɗi mutane kan zama a wajen da yake da ƙarancin iska.

Gwamnatin Jihar Gombe, ta tabbatar da mutuwar mutum uku daga cikin 33 da suka kamu da cutar sanƙarau a jihar.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Habu Dahiru ne, ya bayyana hakan yayin ƙarin haske game da ɓullar cutar a jihar.

Yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, ya bayyana cewa an samu rahoton mutum 53 da ake zargi sun kamu da cutar a ƙananan hukumomi hudu: Kaltungo, Yamaltu Deba, Billiri, da Gombe.

A cewarsa, an tabbatar da mutuwar mutum uku daga ƙananan hukumomin Kaltungo, Yamaltu Deba, da Billiri.

A Shongom kuwa, daga cikin mutum huɗu da ake zargi sun kamu da cutar, an tabbatar da uku na ɗauke da ita.

Sai kuma ƙananan hukumomin Dukku da Nafada, inda aka samu mutum ɗaya kowanne, amma ba a tabbatar da sun kamu ba.

Kwamishinan, ya ce gwamnatin Gombe, ta samar da magunguna kyauta domin kula da masu cutar a cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a ƙananan hukumomi 11 na jihar.

Ya bayyana cewa alamomin cutar sun haɗa da zazzabi, ciwon wuya, da ciwon kai mai tsanani.

Ya kuma shawarci jama’a da su kiyaye tsafta, guje wa zama a ɗakuna marasa iska, da kuma nisantar masu alamomin cutar domin hana yaɗuwarta.