✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargowa

A farkon shekarar 2015, lokacin da yakin neman zaben shugabancin kasar nan ya yi zafi ainun, wadansu  takadararrun yankin Neja Delta, irin su Mujahid Asari…

A farkon shekarar 2015, lokacin da yakin neman zaben shugabancin kasar nan ya yi zafi ainun, wadansu  takadararrun yankin Neja Delta, irin su Mujahid Asari Dokubo da kuma Tompolo, sun fito fili kiri-kiri, suka ce muddin aka kayar da gwarzonsu, kuma dan uwansu, Shugaba Goodluck Jonathan, to Najeriya za ta yi wa kowa kunci, kuma na lahira zai fi al’ummomin cikinta jin dadi, domin kuwa za su tsokalo sama da kara, ta fado, ta murkushe kowa.