Shugaban Ghana a wannan Litinin ɗin ya bayyana ɗaukar mataki kan ministoci da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa fiye da 40 da suka gaza bayyana kadarorin da suka mallaka.
Wannan na zuwa ne a yayin da Shugaba John Mahama ke ci gaba da zage dantse wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar da ke yammacin Afirka.
A yayin karɓar rantsuwar kama aiki a watan Janairun bana ne Shugaban Ghana ya sha alwashin yaƙi da rashawa domin fitar da ƙasar daga ƙangin matsalar tattalin arziki
A watan Afrilun da ya gabata ne mahukunta suka gurfanar da wani babban jami’in tsaro kan wawure miliyoyin daloli daga wata kwangilar tsaron yanar gizo.
Sai dai ana ganin matakin da Shugaba Mahama ya ɗauka wani babban yunƙuri ne na ladabtar da jami’an gwamnati.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa muƙarraban gwamnatin da aka samu da laifin rashin bayyana kadarorin da suka mallaka ba za a biya su albashi ba har na tsawon watanni huɗu.
Bayanai sun ce a ranar 31 ga watan Maris ne wa’adin bayyana kadarorin da muƙarraban gwamnatin suka mallaka ya cika, inda za a hana su albashinsu na watanni huɗu.
Sai dai za a riƙe albashinsu na watanni uku a matsayin ladabtarwa yayin da albashin wata ɗaya zai zama gudunmawar da aka tilasta musu domin kafa sabuwar Hukumar Kula da Asusun Lafiya ta Ghana Medical Trust Fund da ake laƙabi fa “Mahama Cares”.
“Ya zuwa rufe aiki a ranar Laraba, 7 ga watan Mayun 2025, duk wanda ya gaza bayyana kadarorin da ya mallaka ya sallami kansa daga nan take” a cewar wata sanarwa da Shugaba Mahama ya yi a birnin Accra.
Sabuwar dokar ta shafi dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa da suka haɗa da ministoci, hadimin shugaban ƙasa da shi kansa shugaban ƙasar.