✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama masu garkuwa da mutane 3 da kuɓutar da wasu

Binciken farko ya nuna cewa sace Baidoo ya samo asali ne daga wata zamba ta soyayya ta Facebook.

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta sashen tawagarta masu tattara bayanan sirri (IRT), ta kuɓutar da wasu ’yan ƙasar Ghana biyu da aka yi garkuwa da su tare da damƙe wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da ke aiki a kan iyakokin ƙasashen duniya.

Rundunar ’yan sandan a ranar Juma’ar  ta ce hakan ya biyo bayan rahoton da aka shigar gaban babban ofishin hukumar a Abuja a ranar 27 ga Afrilu, 2025, game da yin garkuwa da wani Anastasia Arthur da aka fi sani da Baidoo, ɗan ƙasar Ghana mai shekara 48.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar, ta bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa sace Baidoo ya samo asali ne daga wata zamba ta soyayya ta Facebook.

Adejobi ya ce ci gaba da bincike na fasaha ya nuna wani muhimmin wuri da ke da alaƙa da waɗanda suka aikata laifin, kuma an tura jami’ai domin ɗaukar mataki cikin gaggawa.

Ya ce, tare da haɗin gwiwa da hukumar ’yan sandan Ghana, jami’an IRT sun gano wata ƙungiyar masu aikata laifuka da masu garkuwan da ke aiki a ƙasashen Ghana da Najeriya.

Ya ce, “Babban nasarar da aka samu a binciken sun haɗa da kama wani Emeka Christian, ɗan Najeriya mai shekara 27 da ke zaune a Bolgatanga, Upper Eastern Ghana, wanda ya amsa laifin karɓar kuɗi cedis GH10,000 a matsayin kuɗin fansa ga wanda aka yi garkuwa da shi ta hanyar asusun wayarsa na Ghana.

“Ya kuma amince da tura Naira kwatankwacin kuɗin zuwa wani asusun bankin Najeriya mallakar wani Peter Okoye.”