✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda John Mahama ya karɓi rantsuwar kama aiki a Ghana

Mahama ya yi alƙawarin daidaita tattalin arziƙin ƙasar da ke cikin wani mawuyacin hali.

John Dramani Mahama, ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Ƙasar Ghana, a karo na uku, a wani biki da aka gudanar a Dandalin Black Star da ke Accra.

Mahama, ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da kashi 56.5 na ƙuri’un da aka kaɗa, inda ya kayar da abokin hamayyarsa, mataimakin shugaban ƙasar, Mahamudu Bawumia, wanda ya samu kashi 41.

A jawabinsa na karɓar rantsuwa, Mahama ya yi alƙawarin magance matsalolin tattalin arziƙi da suka addabi ƙasar.

Ya kuma ce zai mayar da hankali kan dawo da martabar tattalin arziƙin ƙasar, da tabbatar da kyakkyawar gwamnati, da yaƙi da cin hanci da rashawa.

Bikin rantsuwar ya samu halartar shugabanni daga ƙasashen Afirka, ciki har da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya halarta domin nuna goyon baya ga sabuwar gwamnatin Ghana.

Mahama, wanda ya taɓa mulkin Ghana daga 2012 zuwa 2017, ya dawo kan mulki ne a lokacin da ƙasar ke fama da matsalolin tattalin arziƙi, ciki har da hauhawar farashi da rashin aikin yi.

’Yan Ghana da dama na fatan cewa sabuwar gwamnatin za ta ɗauki matakan da suka dace wajen farfaɗo da tattalin arziƙi da inganta rayuwar al’umma.