’Yan fashi sun harbe mafarauta da fararen hula kimanin 19 har lahira a Karamar Hukumar Alƙaleri ta Jihar Bauchi.
A yayin ziyarar da ya kai wurin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin yin cikakken bincike da kuma tura karin jami’an tsaro yankin.
Mazauna kauyen Mansur sun ce an kashe ’yan farauta guda tara da kuma fararen hula guda goma, kuma an yi jana’izar ’yan bangar a kauyen Mansur kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Amma ’yan sanad da jami’an Ƙaramar Hukumar Alƙaleri ba su ce komai ba kan adadin mamatan ba.
Kakakin ’yan sanda na jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce kwamishinan ya tattauna da masu ruwa da tsaki a yankin, inda ya buƙaci jama’a kwantar da hankalinsa, ya kuma kasance a cikin shiri, tare da bai wa ’yan sanda goyon baya wajen gudanar da binciken su.
- Kwankwaso: Abba ya mayar wa Baffa Bichi martani
- Umaru ’Yar’adua da shugabannin Najeriya da suka rasu a kan mulki
- NAJERIYA A YAU: Abin da ke kai matasan Najeriya ci-rani wasu ƙasashen Afirka
Wakil ya ce, “A ranar 4 ga watan Mayu, 2025 mun samu rahoto cewa tawagar hadin gwiwar mafarauta daga Duguri da Gundumar Gwana, da ke sintiri a kan hanyar Duguri, Mansur, da dajin Madam da ke kan iyakar jihar Bauchi da Filato, sun yi araba da ’yan fashi, inda a arangamar aka kashe mutane da dama daga bangarorin biyu.
“Mun tura tawagar jami’an tsaro wurin, inda suka gano gawarwakin jami’an tsaro da fararen hula daga kauyen Sabuwar Sara, wadanda ’yan fashin suka harbe su a yayin da suke kokarin tserewa daga harin suka mutu.
“Rundunar ta tura tawaga ta musamman domin kamo duk masu alaƙa da wannan aika-aika.”
Ya kuma ba da tabbacin cewa za a yi bincike cikin gaskiya da adalci domin gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban ƙuliya.