Uwar Gidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta garkame shafinta na Twitter bayan caccakar da take sha kan zargin dauke wani dalibi da ya yi mata kalaman batanci a shafukan sada zumunta.
Wannan na zuwa ne bayan yadda dubban masu amfani da shafukan sada zumunta a Najeriya da ketare ke ta yin fashin baki kan lamarin da ya faru tsakanin Aisha Buhari da dalibin mai suna Aminu Adamu Mohammed da ke Jami’ar Tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa.
- An daure wani mutum wata 4 kan satar ‘cingam’ a Abuja
- An fara ba ma’aikata mazan da matansu suka haihu hutun kwana 14 a Najeriya
Mutane da dama sun bayyana ra’ayinsu kan dauke dalibin, inda wasu ke ganin akwai rashin adalci a lamarin.
Wasu kuma na ganin cewar akwai bukatar a bari shari’a ta yi aikinta a kan dalibin da Uwar Gidan Shugaban Kasa ke ganin ya ci zarafinta.
Tun da farko dai dalibin ya yi amfani da shafin Twitter wajen wallafa cewar “Su mama an ci kudin talakawa an koshi.”
Wasu rahotanni da ba a tabbatar da ingancinsu ba, sun ce wasu jami’an tsaro ne da ake kyautata zaton DSS ne suka yi awon gaba dalibin zuwa Fadar Shugaban Kasa, inda aka dinga jibgarsa, har sai da ya fita daga hayyacinsa.
Sai dai bayan abubuwa sun yi kamari, Kungiyar Dalibai ta Kasa (NAN), ta aike da sakon bayar da hakuri ga A’ishan kan cewar ta yafe wa dalibin a matsayinta na uwa.
Wannan lamarin dai ya yamutsa hazo, inda wasu ke amfani da damar wajen bayyana bacin ransu musamman, ga gwamnatin APC, wadda wasu ke ganin ta gaza a wasu wurare.