Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sallami Manajan Daraktan Bankin Rancen Noma (NIRSAL) daga aikinsa.
Ana hasashen sallamar Aliyu Abdulrasheed daga shugabancin NIRSAL ba zai rasa alaka da zargin almundahana a hukumar ba.
- Aisha Buhari ta janye karar dalibin da ya tsokane ta
- Wike da Ortom sun kalubanci Buhari ya fallasa gwamnonin da ke sace kudaden kananan hukumomi
A watan Janairu, wani binciken kwakwaf da kafar Daily Trust ta yi ya bankado yadda wasu jami’an Hukumar NIRSAL suka hada baki da wasu kamfanoni uku da bankin ya ba wa rancen noman ranin alkama mai fadin kadada 20,000 a jihohin Kano da Jigawa suka karkatar da kudaden.
Tun a lokacin Aliyu Abdulhameed ya musanta zargin da cewa ba shi da tushe kuma an kitsa ne domin bata sunansa da na hukumar.