✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Ya Isa: Shugaban PDP Damagun ya musanta zargin yi wa APC aiki

Wasu masu ruwa da tsaki a PDP na zargin cewa Damagun da  yi wa jam'iyyar zagon ƙasa APC, shi ya sa yake rura wutar rikicin…

Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Umar Iliya Damagun, ya yi Allah Ya isa ga masu zargin da yi wa jam’iyya mai mulki, APC, aiki.

Wasu masu ruwa da tsaki a PDP na zargin cewa Damagun da  yi wa jam’iyyar zagon ƙasa APC, shi ya sa yake rura wutar rikicin cikin gida da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a PDP.

Amma a yayin wata hira da ya yi da BBC, Damagun ya yi fatali da zargin, yana mai cewa Allah Zai saka masa tsakaninsa da masu yi masa wannan ƙazafi.

“Allah Ya isa tsakanina da duk wanda ya yi min wannan ƙazafi, kuma Allah Zai yi mana shari’a,” in ji shugaban na PDP, wanda ake zargi da zama ɗan-amshin-shatan APC.

Ya ce, “Da zan shiga Jam’iyyar APC, da tun lokacin Buhari na shiga,” in ji shugaban na PDP, wanda ake zargi da zama ɗan-amshin-shatan APC.

“Tun da na shiga jam’iyyar PDP a 1999 ban taɓa sauya sheƙa ba. Dole wanda ba ya so na zai nemi yadda zai yaɓa min zargi don ya samu biyan buƙatarsa. Na ce ma na je na yi mitin da Tinubu, a Ingila, wannan duk masu yin wannan na bar su da Allah,” in ji shi.

Dangantaka da Wike da sauya sheƙar mambobi

Dangane da zargin sa da kusanci da kuma alaƙa da Ministan Abuja kuma tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, da kuma yi wa PDP zagon-ƙasa, Damagun ya mayar da martani da cewa: “Duk masu zargin yau ina alaƙa da Ministan Abuja, kan na san shi ko na yi alaƙa da shi, da yawansu sun yi alaƙa da shi. Ni dai laifina guda ɗaya a nan shi ne ban yardar musu yadda suke so su yi da shi ba.”

Game da yadda wasu manyan jaga-jigan jam’iyyar suka koma jam’iyyar APC, Damagun ya ce sauya sheƙar ta ba wa jam’iyyar PDP takaici, duk da cewa babu laifin da aka yi wa masu ficewan.

Ya ce amma duk da haka jam’iyyar tana ƙoƙarin dinke ɓarakar da ta kunno kai a cikinta.

“Yawanci al’amari yana tasowa idan mutum abubuwa suka faru zai nemi dalili da zai ce shi ya tafi,” kamar yadda ya bayyana

“Babu wanda zai ce PDP ta masa laifi”

Damagun ya bugi ƙirji da cewa duk waɗanda suka sauya sheƙa, babu wanda zai iya fitowa ya ce jam’iyyar ta yi masa wani laifi: “Sai dai ma ta yi musu riga ta yi musu wando.”

Ya jaddada cewa PDP ba ta da wata matsala da har ta kai a yi ɓangarori a cikinta.

Amma ya tabbatar da cewa suna da matsalolin cikin gida, domin jam’iyya ba ta taɓa rasa matsala, saboda shugabannin da mambobinta duk mutane, kuma kowa yana da buƙatunsa.

Don haka dole a samu saɓani, a kuma samu son kai, ta yadda wani idan ba a yi masa yadda yake so ba, “to kai ba ka iya ba,” in ji shi.