✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin N37bn: Yadda Sadiya Umar-Farouq ta kwana a hannun EFCC

Tsohuwar ministar jinkai, Sadiya Umar-Farouq ta kwana a ofishin Hukumar EFCC, inda ka titsiye ta kan badaƙalar Naira biliyan 37.

Tsohuwar Ministar Jinkai, Sadiya Umar-Farouq ta kwana a ofishin Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), inda aka titsiye ta, kan badaƙalar Naira biliyan 37.

A daren Lainin Wani jami’in EFCC da ya shaida wa wakilinmu cewa ba shi da izinin yin magana a hukumance ya ce tsohuwar ministar, wadda suka shafe sa’o’i suma mata tambayoyi za ta kwana ofishin hukumar ne domin ta ba da karin cikakkun bayanai da suka dace kan badaƙalar.

Ya ce, “Tana ba hukumar hadin kai a binciken inda take ba mu bayanan da suka dace,” inda take yin karin haske bayanan da ke cikin wasu takardu da ke hannun hukumar da kuma wadanda ta zo da su kamar yadda aka umarce ta.

EFCC ta tistsiye tsohuwar ministar ce kan badaƙalar N37,170,855,753.44 da ake zargin an karkatar a karkashin kulawarta ta hannun wani dan kwangila mai suna James Okwete. Sadiya dai ta musanta sanin dan kwangilar ko yin wata hulda da shi.

A safiyar Litinin ne safiya Umar-Farouq ta kai kanta ofishin hukumar bayan rashin lafiya ya hana ta samun amsa gayyatar hukumar na ranar Larabar da ta gabata.

A makon jiya ne EFCC ta ga gayyaci tsohuwar ministar bayan wani bincike da hukumar ta kaddamar kan ayyukanta a ma’aikatar.

Wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa kafin nan hukumar ta gayyaci wasu jami’an da suka yi aiki da ita a lokuta daban-daban domin su yi bayani kan yadda al’amuran suka gudana a ma’aikatar a shekaru shida da suka gabata.

Kokarin wakilinmu na yin magana da kakakin hukumar, Dele Oyewale bai samuu ba, saboda  kiran da aka yi wa wayar jami’in bai shiga ba, sannan har yanzu bai a amsa sakon tes da aka aika masa ba.