✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta umarci Gwamnati ta biya Emefiele diyyar N100m

Kotu ta hana gwamnati ko hukumominta sake tsare Emefiele ba tare da samun izinin yin hakan daga kotu ba

Kotu ta umarci Gwamnatin Tarayya da Hukumar yaki da Masu Karya  Tattalin Aziki (EFCC) su biya tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele diyyar Naira miliyan 100 kan tauye hakkinsa.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, cewa Mai shari’a Olukayode Adeniyi na Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya ne ya ba da umarnin a ranar Litinin, inda ya kuma hana gwamnati sake tsare Emfiele ba tare da samun izinin yin hakan daga kotu ba.

Emefiele wanda ke fuskantar shari’a kan badakalar kudi, ya maka Gwamnatin Tarayya, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF) da EFCC a kotu ne, kan tauye masa hakkokinsa na rayuwa, walwala, ’yancin kansa, da kuma na damar bayani.

Tsohon gwamnan CBN din ya bukaci alkalin ya umarce su su biya shi diyyar Naira biliyan daya kan tauye masa hakkokinsa.

Emefiele ya tunatar da kotu cewa tsare shi da EFCC da gwamnati suka yi daga ranar 10 ga Yuni, 2023 zuwa 26 ga Oktoba, 2023 ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba haramun ne.

Ya kara da cewa saba umarnin kotu da dama na a sake shi da wadanda ake karan suka yi, take hakkinsa ne na rayuwa, ’yancin kai da walwala, wadanda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da kuma kundin tsarin mulkin dan Adam na Afrika suka tabbatar.