✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta gayyaci Betta Edu kan badakalar kudin tallafi

EFCC ta gayyaci Ministar Jinkai, Betta Edu, wadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar kan badakar kudi Naira miliyan 585

Hukumar yaki da masu karya tattalin arziki (EFCC) ta gayyaci Ministar Jinkai, Betta Edu, wadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar kan badakar kudi Naira miliyan 585.

Gayyatar ta zo kasa da mintuna 30 da Bola Tinubu ya sanar da dakatar da Betta Edu ta hannun kakakinsa, Ajuri Ngelale.

Wani jami’in EFCC ya tabbatar wa da wakilinmu cewa, “Tuni aka aike mata da takardar gayyata a hukumance, kuma muna sa ran za ta zo domin kara haske kan. Don haka muna sa ran zuwa nan ba da dadewa ba,” in ji  wani jami’in na EFCC.

“Binciken da muke yi kan zargin ba zai yi tasiri ba idan ba a dakatar da ministar ba, domin dakatarwar za ta ba mu ’yancin yin aikinmu sosai, yadda shugaban kasa ya umarce mu,” in ji shi.

Jami’in ya shaida wa Aminiya cewa tun da farko hukumar ta bayar da shawarar dakatar da Betta Edu domin ba da damar gudanar da bincike kan badakalar kudin.

Majiyar ta ci gaba da cewa, hukumar ta fara aikin bincike ne nan take bayan shugaban kasar ya sa a gudanar da cikakken bincike kan zargin biyan tallafin Naira miliyan 585.189 da aka ware wa marasa galihu a jihohin Akwa Ibom, Kuros Riba, Ogun da Legas zuwa wani asusu na sirri.

Ba mu samu jin ta bakin kakakin EFCC, Dele Oyewale game da lamarin ba, saboda bai amsa kiran da wayar wakilinmu  ba.

Kungiyoyin farar hula, lauyoyin masu fafutuka, jam’iyyun adawa da sauransu sun yi ta kira da a sallam Beta kan badakalar.