✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya dakatar da Ministar Jinkai, Betta Edu kan badakalar N585m

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Ministar Jinkai, Betta Edu daga mukaminta nan take, kan zargin badakalar kudi

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Ministar Jinkai, Betta Edu daga mukaminta nan take, kan zargin badakalar kudi da ya dabaibaye ofishinta.

Tinubu ya umarci Betta Edu ta mika ragamar jagoranci ga Babban Sakataren ma’aikatar, sannan ta fuskanci bincike a hannun hukumomin da ke da alhakin hakan.

Sanarwar da kakakin shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya fitar ta kara da cewa Tinubu ya nada Ministan Kudi, Wale Edun, ya jagoranci gudanar da cikakken bincike kan badakalar nan take.

A cewarsa, an dora wa kwamitin na Wale Edun alhalin bankadowa da toshe duk wata kofa da ake karkatar da kudade a ma’aikatar, da kuma dawo da kimar gwamnati a idon al’ummar kasa.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan ba shugaban kasan a jawabinsa na sabuwar shekara ya sha alwashin hukunta duk jami’in gwamnatinsa da aka samu da aikata ba daidai ba.

Wanndan badakala dai na da alaka ne da wasu kudade Naira miliyan 585 da Beta Edu ta bukaci Akanta-Janar na Kasa ya tura asusun wani, wanda ofishin Akanta-Janar din ta ce ba daidai ba ne.

Dakatacciyar ministar ta ce kudaden na tallafi ne wasu jihohin kudu, amma ofishin ya ce ba zai yi ba, domin ba ya sanya kudade a asusun daidaikun mutane.

Wasu takardu kuma na yawo da ke nuna ministar da ba da izinin biya alawus din hawa jirgin sama domin tafiyar aiki zuwa filin jirgin sama da babu shi a Jihar Kogi.

Wannan almarin dai ya jawo kiraye-kirayen bincike da kuma dakatar da ita da kuma gudanar da  cikakken bincike.