A yayin da ake ci gaba cece-ku-ce a kan sanar da bullar cutar coronavirus a jihar Kogi, gwamnatin jihar ta sanya dokar kulle a karamar hukumar Kabba, inda wanda ake zargin ya harbu da cutar ya fito.
Gwamna Yahaya Bello ya bayar da umurnin rufe yankin Kabba baki daya a wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Litinin a birnin Lokoja inda ya ce dokar zata fara aikin a daren ranar Talata.
Gwamna Bello ya kara da cewa dokar kullen za ta ba gwamantin jihar damar bin gida-gida domin gudanar da gwaje-gwaje a kan mazauna yankin saboda dakile ‘kudurin wasu da suke neman yada cutar’ a jihar.
• A karon farko, an sami bullar Coronavirus a Kogi
• ‘Yadda mu ka katange jihar Kogi daga COVID-19’
Ya ce gwamnatin jihar na shirye-shiryen samar da tallafi ga mazauna yankin saboda rage musu radadin da dokar za ta yi a kansu inda za a tura jami’an tsaro saboda tabbatar da jama’a sun martaba dokar.
Bukatar daukar mataki
Yahaya Bello ya kara da cewa akwai bukatar a dauki matakan kariya saboda abinda ya kira yunkurin wasu na neman yada cutar a jihar.
Ya bayyana cewa, Kwamitin dakile yaduwar cutar a jihar na bibiyan iyalan wadanda abun ya shafa inda ta gudanar da gwaje-gwaje a kan mutane 13 wanda sakamakonsu ya nuna ba sa dauke da cutar.
Ya bukaci Cibiyar Kulada Lafiya ta Tarayya (FMC) da ta killace likitocinta da suka yi mu’amala da wadanda cibiyar ta bayyana cewa suna dauke da cutar.
Aminiya ta rawaito cewa mutanen da aka sanar sun harbu da cutar dai sun hada da wani uba da dansa tare da wasu shugabannin gargajiya a yankin.
Cece-ku-ce kan coronavirus
Duk da haka gwamnan ya dage cewa har yanzu babu cutar coronavirus a jiharsa ya zargi Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) da sanar da ‘alkaluman bogi’.
Yahaya Bello ya kara da cewa akwai bukatar a dauki matakan kariya “saboda yunkurin wasu na neman yada cutar” a jihar.
Bello ya kara da cewa, siyasantar da lamarin na jihar Kogi ne ya sa ya cije a kan matsayinsa na zargin wasu ‘yan siyasa ne suke bayan alkaluman bogi da Hukumar NCDC ta ke sanarwa a kullum.
Ya jaddada cewa alkaluman da aka sanar a jiharsa na cikin irin wadannan alkaluman da ake siyasantarwa.
Shakku
Gwamnan ya kara da cewa yadda aka dauki daya daga cikinsu wanda ake tunanin zuma ce ‘ta harbe shi’ zuwa wani abun shakka ne.
“Wani abun shakka a lamarin shi ne sanarwar da NCDC ta yi na cewa wani shugaban gargajiya a yankin da dansa sun harbu da cutar.
“Shi ma yaron da aka sanar da cewa ya harbu da cutar yana cig da yawon aike wa mahaifinsa a maimakon a kaishi cibiyar killace wadanda suka harbu da cutar kamar yadda hukumar ta NCDC ta zayyana” Inji Gwamnan.
Ya bukaci al’ummar jihar da su kwantar da hankulansu da kuma daukar matakan kariya saboda kare kansu daga harbuwa da cutar.