✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaratan ‘yan kwallon duniya da asalinsu ’yan Najeriya ne

Idan ana maganar fitar da zaratan matasan ’yan kwallon kafa a duniya, Najeriya ba kanwar lasa ba ce, domin idan Najeriya ba ta zo ta…

Idan ana maganar fitar da zaratan matasan ’yan kwallon kafa a duniya, Najeriya ba kanwar lasa ba ce, domin idan Najeriya ba ta zo ta daya ba, dole ta kasance a cikin na ukun farko.

Duk da cewa akwai damuwa, musamman na yanayin da ’yan wasan Najeriya ke karfon kifi, inda ba su cika dadewa suna haskawa ba.

A lokuta da dama, sukan fito da karfinsu, amma cikin kankanin lokaci sai a neme su a rasa, abin kamar almara.

Daga cikin ’yan wasan da suke dan dade ana jin doriyarsu, akwai Mikel Obi duk da cewa shi ma yakan yi kwan-gaba-kwan-baya, sai Obafemi Martins da Kanu da wasu kalilan.

A yanzu Super Eagles na da zaratan matasan ’yan kwallo, irinsu Samuel Chukwueze da Simon Moses da John Aribo da Victor Oshimhen da sauransu, amma kasar na fama da rashin fitattun ’yan wasan da duniya ke ji da su, duk da kasancewarta daya daga cikin kasashen masu fitar da ’yan wasa

Abin takaicin shi ne, yadda wasu ’yan asalin Najeriya ke wakiltar wasu kasashen duniya, kuma tauraronsu ke haskawa a duniyar kwallon kafa.

Hakan ya sa Aminiya ta rairayo wasu zaratan ’yan wasa da tauraronsu ke haskawa a duniyar kwallon kafa ta yanzu, wadanda kuma asalinsu ’yan Najeriya ne.

ROSS BARKLEY: Ingila da Chelsea

Dan wasan tsakiyan kungiyar Chelsea, Ross Barkley mahaifinsa mai suna Peter Effanga dan Najeriya ne. Yanzu haka yana wakiltar Chelsea ne, kuma duk mai kallon Firimiyar Ingila zai yi wuya bai san sunansa ba.

Ross Barkley, dan wasan Chelsea                                 Hoto: Intanet

DAVID ALABA: Austria da Bayern Munich

Dan wasan bayan Bayern Munich, David Alaba yana daya daga cikin taurarin ’yan wasa da zamani ke yi da su.

Mahaifinsa dan Najeriya ne, kuma ana kiransa da suna Olatokunbo na Yarbanci.

A kakar 2012/2013 da Bayern Munich ta lashe gasar Kofin Zakarun Turai (UEFA Champions League), an nuna Alaba rike da tutar Najeria da ta kasar da Austria da yake wakilta. Sannan ya taba bayyana cewa ya so ya wakilci Najeriya a gasar ’yan kasa da shekara 17.

David Alaba                      Hoto: Shafin Tiwita

Dele Alli: Tottenham da Ingila

Asalin suna mahaifinsa Bamidele, wanda sunan Yarbawa ne, amma mahaifiyarsa ’yar Ingila ce.

A shekarar 2015, wani tsohon dan wasan Ingila wanda shi ma asalinsa dan Najeriya ne, John Fashanu ya so ya jawo hankalin Dele Ali da ya zo ya buga wa Najeriya, amma abin ya ci tura.

Dele Alli dan wasan Tottenham                                                                               Hoto:skysports.jpg

Tammy Abraham: Chelsea da Ingila

Asalin sunansa Kevin Oghenetega Tamaraebi Bakumo-Abraham, kuma a kwanakin nan ma an ta yin magana yiwuwar kiransa ya bugawa Najeriya, amma ya ci tura, duk da kasancewar mahaifinsa, wanda dan Najeriya aboki ne ga Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Najeriya NFF.

Bayan tata-burza da aka yi, daga sai ya zabi ya wakilci Ingila.

Tammy Abraham dan wasan Chelsea                           Hoto: gettyimages.jpg

Jordon Ibe:  Bournemouth da Ingila

Asalin sunansa Jordon Ashley Femi Ibe, kuma mahaifinsa dan Najeriya ne. Yanzu haka yana cikin zaratan ’yan wasan kungiyar Bournemouth.

A shekarar 2015, kocin Najeriya Sunday Oliseh ya yi kokarin jawo hankalinsa y bugawa Najeriya, amma abin ya ci tura.

Jordon Ibe dan wasan Bournemouth             Hoto: Intanet

Fikayo Tomori: Chelsea da Ingila

Asalin sunansa Oluwafikayomi Oluwadamilola “Fikayo” Tomori, kuma iyayensa ’yan Najeriya ne, aka haife shi a Canada, sannan ya girma a Ingila.

Ya wakilci kasar Canada a wasannin kasa da shekara 17 da 20, amma daga bisani ya zabi ya koma Ingila da taka leda, duk da cewa Najeriya ta yi kokarin daukansa.

Fikyo Tomori Hoto: skysports.jpg

STEFANO CHUKA OKAKA: Italiya da Udinese

Dan wasan gaban Udinese STEFANO CHUKA OKAKA, iyayensa baki daya ’yan Najeriya, amma ya samu tikitin zama dan kasar Italiya a shekarar 2007. Sannan a shekarar 2009 ya wakilci kasar a gasar ’yan kasa da shekara 19.

Yanzu haka yana taka leda ne da kungiyar Udinese na rukunin Seria A na Italiya.

Sidney Sam: Jamus da SCR Altach

Tsohon dan wasan Bayern Liverkusen, wanda ya yi fice a taka leda a tsakiya, shi ma mahaifinsa dan Najeriya, amma taba bugawa Najeriya ba.

A lokacin da Samson Siasia ke kocin Najeriya, ya yi kokarin dauko Sam ya bugawa Najeriya, abin ya ci tura, inda ya ce ya kira sama da sau 10, sannan ya tura masa sako, amma bai amsa ba.

Akwai wasu da dama da suke bugawa wasu kasashen da ba su yi fice ba, kamar su Emma Sarki da ya bugawa Najeriya a wasannin kasa da shekara 17 da 20 da 23, amma daga baya ya koma Haiti da Oguchi Onyenwu da yake bugawa Amurka, da Nedum Onuoha da ke bugawa Ingila da sauransu.