Majalisar Wakilai ta yi watsi da kudurin dokar da ke neman sanya tsarin mulkin karba-karba a tsarin shugabancin Najeriya.
Kudurin dokar na neman yi wa kundin tsarin mulki na 1999 gyaran fuska domin ba da damar yin karba-karbar kujerar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a tsakanin yankunan siyasan Najeriya guda 10.
Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Benjamin Okezie Kalu ne ya gabatar da kudurin, wanda ke cikin jerin sauye-sauye bakwai a kundin tsarin mulki da majalisar ta tattauna a kansu a zamanta na ranar Talata.
Muhawarar da aka tafka
Bayan gabatar da kudurin a zaman da Kalu ya jagoranta, Honorabul Aliyu Madaki (NNPP, Kano), ya soki kudurin da cewa tsarin raba-daidai na kasa ya riga ya magance duk abubuwan da kudurin ke nema.
- HOTUNA: Trump na ziyara a Saudiyya
- Yadda ISWAP ta kashe sojoji ta kwashe makamai a sansanin soji a Borno
- Bom ya kashe jami’an ilimi 2 a Borno
Aliyu Madaki ya ci gaba da cewa batun karba-karba, abu ne da ya kamata a bar wa jam’iyyun siyasa su tsara wa kansu idan sun ga dama, amma babu bukatar mayar da shi doka a cikin kundin tsarin mulki.
Amma a martaninsa, Honorabul Ali Isah (PDP, Gombe) ya bayyana cewa yin dokar mulkin karba-karba a kundin tsarin mulkin zai tabbatar da adalci ta yadda kowane yankin kasar zai ji cewa ana damawa da shi, ba a mayar da shi saniyar ware ba.
Sai dai kuma, Honorabul Sada Soli (APC, Katsina) ya bayyana cewa “kudurin zai yi mummunar illa ga hadin kan kasar nan,” Ya kara da cewa karba-karba zai takaita zabin da al’ummar Najeriya ke da shi kuma zai iya jefa kasar a hannun marasa kwarewa.
Amma Honorabul Kalu, wanda ya jagoranci zaman na ranar Talata, ya mayar da martani da cewa kowane yanki a kasar yana da mutanen da ke da gogewar da za su iya shugabantar kasar cikin kwarewa.
Ya bayyana cewa manufar kudurin nasa ita ce samar da tsarin da zai ba da cikakkiyar damar yin shugabanci ga kowane shiyya a kasar, ta yadda za ta ba da gudummawarta wajen kawo ci-gaba.
Sai dai kuma Honorabul Shina Oyedeji ya kalubalance shi da cewa, manufar tsarin dimokuradiyya ita ce bayar da cikakkiyar damar yin gasa mai tsafta, saboda haka, yin dokar mulkin karba-karba ya ci karo da manufar dimokuradiyya.
Ya ce, don haka, “Ya kamata a ba wa kowa damar yin takara a kowane mataki da kuma lokaci.”
Shi ma Honorabul Bello El-Rufai (APC, Kaduna) a yayin da yake fatali da kudurin, ya bayyana cewa yin dokar mulkin karba-karba a kundin tsarin mulkin Najeriya, babu abin da zai haifar sai kiyayya ta kabilanci, duba da yawan al’ummomin da ke kasar.
Bayan sauraron bangarorin da suka tafka muhawarar, Mataimakin Shugaban Majalisar ya sa a yi kuri’a ta hanyar murya a zauren majalisar, inda masu adawa da kudurin suka samu rinjaye.