Mamba a Kwamitin Amintatttun Jam’iyyar PDP, Farfesa Alphonsus Nwosu, ya fice daga jam’iyyar.
Farfesa Alphonsus Nwosu tsohon Ministan Lafiya ne kuma na hannun daman dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
- Sabbin katinan zabe 13m muka buga —INEC
- Gobe za a yi ganawar kai tsaye da ’yan takarar Gwamnan Katsina
Ya bayyana rashin bin tsarin karba-karbar takarar shugaban kasa a PDP a matsayin dalilinsa na raba gari da ficewarsa ita.
Tuni dai ya aike wa Shugaba PDP na Ƙasa, Iyorchia Ayu da Shugaban Riko na Kwamitin Amintatttun jam’iyyar, Adolphus Wabara da kuma shugaban mazabarsa takardarsa ta ficewa daga jam’iyyar.
Farfesa Nwosu na daga cikin iyayen PDP da aka kafa a ta da su.
Ya kuma taka muhimmiyar rawa a mukaman jam’iyyar da ya rike a matakin kasa da kuma yankin Kudu.