✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zanga ’Yancin ’Yan Najeriya ne —Kungiyar Arewa

Kungiyar Fafutikar Sake Farfaɗo da Arewa ta bayyana goyon bayanta ga shirin zanga-zangar yaki da tsadar rayuwa a Najeriya.

Kungiyar Fafutikar Sake Farfaɗo da Arewa ta bayyana goyon bayanta ga shirin zanga-zangar yaki da tsadar rayuwa a Najeriya.

Kungiyar ta ce tana da yakinin cewa matakin wannan zanga-zanga da ke tafe zai kawo sauyin da ake matukar buƙata a kasar.

Sakataren kungiyar, Dokta Salisu Nani Zigau, ya bayyana cewa dokar kasa ta ba ’yan Najeriya ’yancin yin zanga-zanga, kuma babbar dama ce gare su ta bayyana bukatunsu da neman adalci da kuma kawo kyakkyawan sauyi.

“Zanga-zangar lumana da ake shirin yi a fadin Najeriya shaida ce da ke nuna ittifaki da kuma jajircewan ’yan kasar domin sama wa kansu da kuma ’ya’yansu ingantacciyar rayuwa a nan gaba.

“Ba sai mun bata lokacin bayyana muhimmancin wannan zanga-zanga a yankin Arewa ba.

“A tsawon lokaci yankin na fama da matsalolin talauci da rashin tsaro da ta’addancin Boko Haram.

“Sauran sun hada da rashin abubuwan more rayuwa ga kuma yara marasa zuwa makaranta,” kamar yadda ya bayyana.

Dokta Salisu Nani Zigau, ya ci gaba da cewa, “Wannan zanga-zangar wata dama ce ga ’yan Arewa su hadu su nuna rashin jin dadinsu da kuma bukatunsu musamman na samun shugabanci na gari da kyawawan tsare-tsare da za su daga daraja da yanayin rayuwarsu da na yankin.”

Ya ce, a don haka, “muna kira ga masu wannan zanga-zanga su kasance cikin lumana da bin doka.

“Sannan muna kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da kungiyoyin fararen hula da su mutunta ’yancin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba masu zanga-zangar na bayyana ra’ayinsu da rashin jin dadinsu ta hanyar lumana.

“Muna kira ga gwamnati ta saurari bukatunsu ta biya musu sannan ta dauki matakan share musu hawaye tare da tafiyar da kowane bangare.

“Ya kamata mu yi amfani da wannan dama mu hada kanmu matsayin ƙasa guda domin samun rayuwa mai inganci a nan gaba.”