’Yan Najeriya sun yi wa Majalisar Dokoki ta Kasa cikar kwari, suna zanga-zanga kan kisan Musulmi kimanin 90 da jirgin soji ya yi a wurin taron Mauludi a Jihar Kaduna.
Masu zanga-zangar sun bukaci Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar da ya magance matsalar tsaro da ke addabar Najeriya ko kuma ya ajiya aikinsa.
“Tun da ministan tsaron nan ya kama aiki matsalar tsaron Najeriya sai kara tabarbarewa take,”, in ji jagoran zanga-zangar, karkashin inuwawr Majalisar Matasan Najeriya (NYCN), Nasir Ishaku.
“Sai rasa sojoji da ’yan sandan Najeriya ake ta yi. Ga daliban jami’o’inmu a hannun yan bindiga, babu wanda ya san inda suke.
- Abin da ’yan Najeriya suke cewa kan Harin Mauludin Kaduna
- Kisan Ummita: Bayan hutun wata 7, an sake dage shari’a zuwa 2024
Ishaku wanda kuma shi ne shugaban kungiyar matasan Arewa, ya ce yaza wajibi a bi wa wadanda aka kashe a harin hakkinsu.
Ya ce yadda ake kashe mutane kullu-yaumin musamman a Arewa, abin da ba za a lamunta ba ne.