Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta shugaban ofishin jakadancin Faransa a kasar bisa tsamin dangantakar da ya biyo bayan zanen batanci ga manzon Allah (S.A.W) da kasar ta yi.
A makon nan ne Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ’yan kasarsa na da ’yancin wallafa kowane irin zanen batanci, kalamin da ya jawo la’anta daga kasashen Musulmai da dama.
- An fille kan malamin da ya yi batanci ga Annabi
- Batanci ga annabi: Shugaban Turkiyya ya bukaci a daina sayen kayan Faransa
Kamfanin Dillancin Labaran Kasar Iran (ISNA) ya rawaito cewa, “Muna Allah-wadai ga kowanne irin batanci ga Ma’aiki da kuma irin matsayar da hukumomin Faransa suka dauka a kan hakan.”
Ma’aikatar ta yi takaicin kan yadda aka keta alfarmar miliyoyin Musulmai da sunan ’yancin fadin albarkacin baki a Faransa.
Iran ta kuma yi gargadin cewa lamarin zai kara rura wutar gaba tsakanin Faransa da sauran Musulmai.
Kafafen watsa labaran kasar sun nuna an shirya gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Faransa a Iran.
Idan dai za a iya tunawa a ’yan watannin baya ne Jaridar Charlie Hebdo ta sake wallafa zanen batanci ga Ma’aiki.
Zanen batancin dai ya janyo Allah-wadai daga al’ummar Musulmin duniya inda har wasu ke kiran a kaurace wa amfani da kayan da aka sarrafa a Faransa a domin ladabtarwa.