Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kakkausan gargaɗi kan barazanar Amurka da ƙawayenta na kai wa ƙasarsa hari.
Khamenei ya sha alwashin maida mummunar martani idan har Amurka da ƙaddamar da hare-hare a ƙasar ta Iran.
Gargaɗin nasa martani ne kan barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa ƙasar cewa za su kai mata hari.
- Muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka kan kashe ’yan Arewa a Edo — Sarkin Musulmi
- Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka
“Suna yi min barazana, kuma idan suka sake suka kawo min hari tabbas zan rama,” in ji shi.
Yayin wata tattaunawa a ranar Asabar ne Trump ya yi alƙawarin kai wa Iran ɗin hari matuƙar ba ta amince da yarjejeniyar makamin ƙare dangin ba.
“Idan ba su amince da sabuwar yarjejeniyar makaman ƙare dangin ba, za mu tada bama-bamai,” in ji Trump.
Sai dai bai bayyana ko Amurkan ce za ta kai harin ba ko kuma ƙawarta Isra’ila.
To sai dai cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, kakakin ma’aikatar wajen Iran Esmaeil Baqaei ya ce barazanar ta Trump a bainar duniya yana matsayin shugaban kasa abin mamaki ne, kuma babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron ƙasa da ƙasa.