✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan yi miki wanki

Wani Bakano ne ya ce wa matarsa: ‘’Ki tattara kayanki kakaf ki tafi gidanku, na sake ki!’’ Ana cikin hakan sai babanta ya kira ta…

Wani Bakano ne ya ce wa matarsa: ‘’Ki tattara kayanki kakaf ki tafi gidanku, na sake ki!’’ Ana cikin hakan sai babanta ya kira ta a waya, sai ta sa muryar wayar a fili, sai babanata yake gaya mata cewa: ‘’Walida, yanzu na turo Aminu da kudi Naira miliyan bakwai, ki dauki Naira miliyan biyu, sai ki ba mijinki Naira miliyan biyar, ya kara jari.” Bakano yana jin haka, bayan ta gama wayar sai ta ce: ‘’To, maigida ni zan tafi.’’ Shi kuwa sai ya ce: ‘’Ina za ki je, ko ba ki ji abin da na gaya miki ba ne? Cewa na yi fa ki tattara kayanki kakaf zan yi miki wanki!”
Daga Malam Babaji Na Khalisa Hadeja, 07068068315