A ranar Alhamis ɗin nan ne rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa, an samu fashewar wani abu a wurin ajiyar makamai da ke barikin Giwa a Maiduguri wanda ya faru sakamakon tsananin zafi da aka samu a yankin.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Kaptin Reuben Kovangiya, a hedkwatar rundunar haɗin gwiwa ta shiyyar Arewa maso gabas ta Operation HAƊIN KAI.
- ’Yan fashin teku sun sace mata 4 a hanyar ruwa ta Bayelsa
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta
Ya fayyace cewa fashewar ta faru ne ba sakamakon wani harin maƙiya ba, illa dai lamarin ya faru ne sakamakon yanayin zafi da ake fama da shi a halin yanzu da ya shafi makaman da aka ajiye a cikin ginin.
“Fashewar ta faru ne saboda yanayin zafi da ake ciki a Maiduguri, wanda ya kai ga fashewar wasu alburusai,” in ji Koɓangiya.
Ya ƙara da cewa, tuni an shawo kan lamarin ba tare da ɓata lokaci ba ta hanyar haɗin gwiwa da jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Borno da sauran sassan bayar da agajin gaggawa daga jami’an tsaro.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “An tura dakarun Operation HAƊIN KAI domin kare jama’a da kuma hana miyagu yin amfani da abin da ke faruwa.”
Don haka rundunar ta buƙaci mazauna yankin da su yi watsi da duk wani jita-jita na kai hari a ƙaramar hukumar Maiduguri kuma su kwantar da hankalinsu akan hakan.
“Don haka ana kira ga jama’a da su yi watsi da duk wani hasashe na harin… kuma su kwantar da hankula,” in ji Koɓangiya.
Rundunar Operation HAƊIN KAI dai na ci gaba da yaƙi da ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas ba dare ba rana.