Mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar PDP, Sanata Bukola Saraki, ya ce zai yi amfani da fasahar zamani wajen magance matsalolin da suka addabi Najeriya in aka zabe shi a 2023.
Saraki ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin da ya ke ganawa da daliget din PDP na Jihar Taraba, a Jalingo, babban birnin Jihar.
- An rufe Kasuwar Dei-dei kan rikicin ’yan acaba da ’yan kasuwa
- Shekara 1 Da Fara Rediyon Aminiya ta Intanet
Ya ce ya je jihar ne domin neman goyon bayan wakilan Taraba don ya zama shugaban Najeriya.
“Kasarmu ta shiga cikin abubuwa da yawa kuma muna bukatar mu yi abubuwa daban-daban don dawo da ita kan saiti.
“Ba za mu sake zabar irin shugabannin da ke mulkin a yanzu ba a nan gaba. 2023 ita ce makomar kasar nan da ‘ya’yanmu.
“Kan wannan kasa ya rabu, don haka ba zamu bari a yi amfani da kuri’a wajen sake raba mu ba.
“Dole ne mu yi abin da ya dace saboda wadanda suka mutu ba tare da sun aikata laifin komai ba.
“Mun sha wahala sosai a kasar nan kuma dole ne mu nemi hanyar ceto Najeriya.
“Ni kadai ne mai burin da ya fito da tsarin siyasa don magance matsalar Najeriya saboda rashin shugabanci na gari ne ake fama da rashin tsaro.
“Muna bukatar shugaban kasa wanda ya fahimci tattalin arziki kuma yana da hangen nesa don saka hannun jari,” inji shi.
Saraki ya kuma yi alkawarin zuba hannun jari a fannin hakar ma’adinai da noma, don samar da karfin gwiwa ga ’yan Najeriya.
A nasa martanin, Gwamna Darius Ishaku na Jihar Taraba, ya ce Saraki yana da kwarewa da jajircewar da zai jagoranci Najeriya.