✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan yi aiki tukuru don cika alkawuran da na dauka —Tinubu

Tinubu ya ce zai yi aiki tare da kowa don tabbatuwar dimokuradiyya a mulkinsa.

Zababben Shugaban Kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin yin aiki tukuru wajen sauke nauyin da rataya a wuyansa tare da tafiya da kowa wajen kawo ci gaban kasa.

Wannan shi ne tabbacin da bai wa ’yan Najeriya a lokacin da shi da mataimakinsa, Kashim Shettima suka karbi takardar shaidar lashe zabe a Cibiyar Taro ta Kasa ICC da ke Abuja a ranar Laraba.

“Zan yi aiki dare da rana. Zan yi iya bakin kokarina wajen ganin Najeriya ta hau kan hanya.

“Wannan nasara ba tawa ba ce ni kadai ko ’ya’yan jam’iyyar APC, nasara ce ga ’yan Najeriya da suka himmatu wajen samar da ci gaba.”

Jawabin Tinubun na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban Kasa da aka gudanar a ranar Asabar.

Tinubu ya samu rakiyar matarsa, Oluremi Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da kuma wasu jiga-jigan jam’iyyar APC.