Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya ce zai tsaya takarar Shugaban Kasa a zaben shekarar 2023 mai zuwa.
Ya bayyana matsayin nasa ne ranar Litinin a Sakkwato, inda ya ce shi ne ya fi cancanta da ya ja ragamar kasar a badi.
- Sa’o’i bayan ayyana neman takara a 2023, EFCC ta sake waiwayar Rochas da sabbin tuhume-tuhume
- Gyaran matatun mai ya lashe N100bn a 2021 – NNPC
Gwamna Tambuwal dai ya taba neman tsayawa takarar gabanin zaben shekarar 2019, amma ya sha kaye a hannun tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, yayin zaben fid da gwani na jam’iyyar PDP.
Ya ce a wannan karon ma, zai sake neman takarar ne a karkashin tutar jam’iyyar ta PDP.
Tambuwal dai ya taba zama Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya tsakanin shekarar 2011 da 2015.