Tsohon Gwamnan Jihar Filato, kuma sanata mai wakiltar Arewacin jihar a Majalisar Dattawa, sanata Jonah Jange ya ce zai iya maye gurbin Shugaba Buhari a 2019.
Tsohon gwamnan ya ce matukar ‘yan Najeriya na bukatar sauyi mai nagarta da aminci, to lallai su ba shi dama ya ja ragamar mulkin kasar a zaben 2019.
Jonah Jang ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Du, a Karamar Hukumar Jos ta Kudu a ranar Lahadin da ta gabata.
"Ina siyasa ne domin taimakon al’umma. Idan har mutane suna so in zama Shugaban Kasa me zai hana ni."