Mayaƙan Boko Haram sun kashe sojoji da ba a san adadinsu ba tare da yin awon gaba da wasu da dama bayan wani ƙazamin hari da suka kai a sansanin soji da ke yankin Marte a Jihar Borno.
Majiyoyin soji sun ce mayaƙan ƙungiyar sun fi karfin sojojin, inda suka kwashi makamai masu tarin yawa sa’annan suka cinna wa ma’ajiyar makamai da ke sansanin sojin wuta.
Mazauna yankin sun bayyana cewa da misalin ƙarfe 3 na asuba, kafin wayewar garin ranar Asabar ne Boko Haram ta ƙaddamar da harin.
Wani soja da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce, “ISWAP ta ƙwace Marte, an kashe sojoji da dama, an kama wasu, amma wasu sun samu sun tsere zuwa Dikwa, inda runduna ta 24 take.
- Ya kashe abokinsa saboda hula a Kano
- NAJERIYA A YAU: Matsalar lantarki: ’Yan Najeriya sun yi tir da biyan diyya ga ’yan Band A
“’Yan ta’addan sun ƙona tankokin yaƙi kuma sun kwashi makamai daga sansanin sojin,” in ji shi.
Wani mazaunin Marte, gari mai nisan kilomita 38 daga Dikwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Dikwa, ya ce sun ji karar harbe-harben kuma daga bisani suka ga jirgin soji yana shawagi.
Ya ce, “mun samu labarin cewa an tura ƙarin jami’an tsaro kuma an ƙwato sansanin sojin, amma ’yan ta’addan sun sun sace makamai kuma sun koma motoci da rumbun makaman sojin da ke wurin.”
Ya ci gaba da cewa, “abin takaici mayaƙan sun tsare mata da ƙananan yara da dama a Sabon Marte, amma wasu da dama sun samu tserewa zuwa Dikwa domin tseratar da rayuwarsu.
“Ba a daɗe ba da ’yan ƙungiyar suka kai hari a Malam Fatori, inda suka kashe sojoji 21 da wani daga cikin kwamdojinmu.”
Daga watan Janairu zuwa yanzu an kai wa sansanonin soji da dama hare-hare a yankin Tafkin Chadi da kuma Dutsen Mandara da ke Dajin Sambisa a jihohin Borno da Yobe.