Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke hukuncin ratayewa ga wani mutum da ta samu da laifin kashe abokinsa saboda hula.
Kotun da ke zamanta a kan titin Miller ta yanke wa mutumin mai suna Adamu Isma’ila Arzai hukuncin ne bayan an gurfanar da shi kan zargin soka wa abokinsa mai suna Auwal Shehu Kabara wuƙa a lokacin da suke faɗa.
A shekarar 2016 ne faɗa ya kaure tsakanin abokan biyu a kan wata hular sanyi a lokacin da suka yi wata tafiyar fatauci a Jihar Bauchi.
A yayin zaman kotun, mai gabatar da ƙara, Wahida Isma’il, ta gabatar da shaidu biyar, shi kuma wanda ake tuhuma ya kare kansa.
- Matashi ya kashe saurayin ƙanwarsa a Kano
- NAJERIYA A YAU: Matsalar lantarki: ’Yan Najeriya sun yi tir da biyan diyya ga ’yan Band A
Bayan sauraron duka bangarorin, alƙalin kotun, Mai Shari’a Muhammad Musa Karaye, ya bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun kawo gamsassun hujjojin da ke tabbatar da cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin.
Daga nan kuma ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.