An gurfanar da wani mutum a gaban kotun Musulunci kan zargin yi wa matar maƙwabcinsa dukan kawo wuƙa a Jihar Kano.
Mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotun da ke zama a unguwar Kurna Asabe cewa wanda ake zargin ya kuma ji wa matar auren munanan raunuka.
Ya yi wa matar wannan aika-aika ne bayan wata taƙaddama, inda ya ji mata munanan raunuka a fuska da wasu sassan jikinta.
Alƙalin kotun, Khadi Alhaji Jibrin Ɗanzaki, ya ba da umarnin tsare mutumin a gidan yari sannan ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 20 ga watan nan na Mayu.