Wasu ma’aikatan lafiya biyu sun rasu, wasu da dama sun jikkata bayan motarsu ta taka bom a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri a Jihar Borno.
Ana zargin mayakan Boko Haram ne suka dasa bom din a wani hari da kungiyar ta kai a kan babbar hanyar a ranar Litinin.
Shaidu sun bayyana cewa, wadanda suka mutun suna zaune ne a gaban motar jigilar mangoro, kirar Toyota Hiace da ta dauko su daga Damboa zuwa Maiduguri.
Sun kara da cewa tashin bom din ya haifar da sabuwar damuwa game da lafiyar matafiya a kan hanyar.
- Yadda ISWAP ta kashe sojoji ta kwashe makamai a sansanin soji a Borno
- ’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 5 a Filato
- Ya kashe abokinsa saboda hula a Kano
Wata majiya a karamar hukumar Damboa ta tabbatar da cewa mamatan jami’an Hukumar Ilimi na Karamar Hukumar Damboa ne.
Tuni jami’an tsaro suka killace yankin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainihin yadda lamarin ya kasance.