Tsohon Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Roy Keane, ya yi barazanar makure wuyan kocin kungiyar, Ole Gunnar Solskjaer saboda ci gaba da sanya dan wasan kungiyar, Fred a wasanni.
Roy Keane ya yi wannan furuci duk da rashin kamatarsa saboda fusatar da ya yi da yadda Solskjaer ya nace wajen fitowa da dan wasan na Brazil a galibin wasannin da kungiyar ke yi kakar bana.
- Kotu ta daure Abdulrasheed Maina shekara 61 kan badakalar fansho
- Dan sanda ya kashe abokan aikinsa 4 a Indiya
Keane ya jefa shakku kan makomar Solskjaer ta ci gaba da jan ragamar horas da ’yan wasa a Old Trafford yayin da yake zanta wa da kafar watsa labaran wasanni ta Sky Sport a karshen makon da ya gabata.
A cewarsa, da a ce Solskjaer zai matso kusa da shi a wannan yanayi na fusata da yake ciki su yi ido hudu da shi, to babu abin da zai hana ya makure wuyansa.
“Duk wanda a wannan hali da ake ciki yana tunanin Fred ya cancanci ci gaba da zama a United, to kuwa yana da nakasu a fahimtarsa.”
Tsohon kocin na kungiyar Nottingham Forest, Ipswich United, Sunderland da kuma Aston Villa, ya bayyana bacin ransa kan yadda Manchester United ta sha kasha a hannun Manchester United da ci 2-0 a ranar Asabar.
Wannan shan kashi da United ta yi ya biyo bayan wanda ta sha a hannu Liverpool da kwallaye 5-0 makonni biyu da suka gabata a Firimiyar Ingila.
Sauran ’yan wasan United da Keane ya bayyana bacin ransa a kansu saboda rashin kwazo sun hada da Harry Maguire, Luke Shaw da kuma golan United, David De Gea.
A caccakar da ya yi, Keane ya tunatar da Solskjaer cewa United ba irin wasu kananan kungiyoyin kwallon kafa bane, wanda dole ne sai ya rika kare martabarta wajen buga wasanni a gida da hakan ne kadai zai iya ba ta damar lashe gasanni.
Yanzu haka Manchester United na matsayi na 6 a teburin Firimiya da maki 17, yayin da Manchester City tare da West Ham ke matsayi na 2 da maki 23, inda Chelsea ke jan ragama da maki 26.