✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan goya wa surukina baya ya zama Gwamnan Imo na gaba – Okorocha

Gwamnan Jihar Imo Mista Rochas Okorocha ya  ce zai goyi bayan surukinsa Uche Nwosu domin ya gaje shi a matsayin Gwamnan Jihar idan ya yanke…

Gwamnan Jihar Imo Mista Rochas Okorocha ya  ce zai goyi bayan surukinsa Uche Nwosu domin ya gaje shi a matsayin Gwamnan Jihar idan ya yanke shawarar tsayawa takara a zaben badi.

Nwosu, wanda a yanzu haka shi ne Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati na Gwamna Okorocha shi ne mijin babbar ’yar Gwamnan mai suna Ulomma.

Ana dai samun karuwar adawa da yunkurin Okorocha na ganin surukinsa Nwosu ya zama Gwamnan Imo a badi.

Wata takardar sanarwa da Babban Sakataren Watsa Labarai na Gwamnan, Mista Sam Onwuemeodo, ya fitar a ranar Litinin da ta gabata, ta ce Gwamna Okorocha ya bayyana wannan kudiri na goya wa surukinsa baya ne a lokacin da shugabannin Jam’iyyar APC daga karamar Hukumar Birnin Owerri suka kai masa ziyara, kuma suka nemi ya karfafa wa surukin nasa ya fito takarar Gwamnan.

Rahotanni sun ce Okorocha ya yi amfani da wannan dama ya rika zuba ruwan yabo ga surukin nasa, inda ya ce, Nwosu ne ya cancanci kujerar kuma bai kamata batun karba-karba ya kawo masa cikas ba.

Nwosu dai ya fito ne daga mazabar Sanata guda da Okorocha, kuma sauran shiyyoyin suna ta neman a gusa da kujerar zuwa shiyyoyinsu.

 “Uche Nwosu yana da kwazon aiki, kuma ba ya gajiya. Matashi ne mai saukin kai. Ba ya da alfahari. Ba ya da  girman kai. Don haka jiji da kai ba zai shiga kansa ba,” inji Okorocha.

Ya ce, “duk da mukamin da yake rike da shi, ba za ka gan shi yana cacar baki da wani ba, ko yana cin zarafin wani. Ba ya nuna bambanci ga kowa, ya alla ka fito ne daga shiyyar Orlu ko Owerri ko Okigwe. Yana hulda da mutane cikin haba-haba.”

“Kuma na bincike ciki da waje; ban samu yana aikata ba daidai ba. Abin da jihar take bukata shi ne Gwamnan Imo ba na shiyyar Owerri ko Orlu ko Okigwe ba.  Shiyya ba za ta kawo abinci kan teburin kowa ba,” inji shi.