✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto mutum 6 daga hannun masu garkuwa a Kebbi

Gwamnatin Kebbi ta bayyana fatan kawar da ɓarayin shanu da ’yan bindigar Lukurawa a yankin Zuru da Argungu.

Wata rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro ta samu nasarar kuɓutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su da shanu da aka sace a Jihar Kebbi.

Bayanai sun ce an sace mutanen da dabbobin ne a ƙauyukan Ukuhu da Kokanawa a Karamar Hukumar Danko Wasagu ta jihar.

Wani daraktan tsaro a Gwamnatin Kebbi, Abdurrahama Zagga ne ya sanar wa manema labarai nasarar da aka samu a ranar Talata, inda ya ce an kai samamen ne bayan umarni da aka samu daga Gwamna Nasiru Idris bisa bayanan sirri da aka tattaro a yankin.

A cewar Zagga, tawagar jami’an tsaro ta fatattaki ’yan ta’addan da suka yi garkuwa da mutanen da kuma shanun da suka sace a wani gulbi da ke iyaka da Jihar Zamfara.

“Mutane da aka ceto an mika su ga iyalansu. Kuma wannan abin farin ciki ne ga gwamna musamman a kokarin da jami’an tsaro suke yi, lamarin da zai kara inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin masarautar Zuru.”

Ya bayyana fatan da suke da shi na kawar da ɓarayin shanu da ’yan bindigar Lukurawa a yankin Zuru da Argungu.