Dan takarar Gwamnan Jihar Katsina a karkashin jam’iyyar PRP, Alhaji Imrana Jino ya yi alkawarin biyar diyyar duk mutanen da ’yan bindiga suka kashe a Jihar muddin aka zabe shi.
Ya bayyana hakan ne a wajen taron al’umma da ’yan takarar Gwamnan Jihar, wanda kamfanin Media Trust, mamallaka jaridar Aminiya suka shirya ranar Asabar a Katsina.
- Direbobi sun saki hanyar Zariya-Kano bayan sun rufe ta tsawon kwana 3
- Tsaron Katsina: Za mu dora daga inda Masari ya tsaya —APC
Ya ce hakan na daya daga cikin manufofinsa na yaki da ayyukan ’yan bindiga da sauran matsalar tsaron da ta addabi Jihar.
Imrana Jino ya kuma ce bai ga dalilin da zai sa a ce akwai gwamnati a Jiha, amma al’ummarta na cikin hali musamman na biyan diyyar sama da Naira milyan ɗ100 don karbo mutun daya, amma ta gaza biyan diyyar wanda aka kashe bz tare da ya san hawa ba balle sauka.
Ku kasance da shafukanmu a dandalin sada zumunta domin jin yadda take kayawa a wajen taron.