Wani zaki ya cizge yatsar ma’aikacin gidan namun daji a lokacin da yake taba zakin a cikin kejinsa da nufin burge masu yawon bude-ido da suke kallo.
Bidiyon wanda aka ce na gidan namun dajin ne da ke kasar Jamaika ne, ya nuna yadda mutumin yake kokarin taba zakin, kamar yadda yake wasa da kyanwa.
- Watan gobe za a dawo haska shirin Labarina
- Dokar hana acaba: Gwamnatin Legas ta ragargaza babura 2,000
Yana cikin wasa da zakin ne sai zakin ya kama yatsarsa ya cizge.
Bayan zakin ya saki hannunsa an ga mutumin ya tashi yana fama da radadi inda ya wuce don ganin likita.
An ga mutumin yana kokarin kwace hannunsa, yayin da zakin ya ci gaba da rikewa.
Ganau sun shaida wa jaridar Jamaica Obserber cewa, hakan ya faru ne a wani rangadi da suke yi a yammacin ranar.
“Lokacin da abin ya faru, sai na dauka wasa ne”, inji wata mata.
“Ban gane muhimmancinsa ba, domin aikinsu ne su yi wasa da dabbobin.
“Tabbas lokacin da ya fadi kasa kowa ya gane cewa da gaske ne,” inji ta.
“An bar masu yawon bude-idon baki bude, cike da mamakin yadda mutumin ya rasa yatsarsa bayan zakin da ke kejin ya cizge ta lokacin da yake wasa da shi. Kowa ya fara firgita.
“Fatar gaba daya da kuma kusa da yatsar sun gutsure,” inji ta.
Jaridar ta tuntubi mahukuntan gidan zoo na Jamaika da ke kusa da Lakobiya, kuma wani ma’aikacinsu ya ce, ba su da masaniya a kan lamarin.
Manajan Daraktar Kungiyar Jama’a don riga-kafin zalunci ga dabbobi na Pamela Lawson ta ce, kungiyarta na duba abin da ya faru.
“Wani mai yawon bude-ido ya ce, mai kula da namun dajin ya yi yunkurin burge masu ziyara, amma ya fusata zakin.
“Ihun da mai kula da dabbobin da ya yi yayin da yake kokarin kwace yatsarsa daga bakin zakin ya gigita jama’a.
“Duk fatar hannun sai da ta cire. Tserewa na yi daga wurin saboda ba na son ganin jini.
“Amma kuma a fuskarsa, tamkar babu alamar yana jin zogi, yayin da yake barin wurin,”inji ta.
“Za mu isa can wurin kuma zan yi magana da Hukumar Kula da Muhalli da Tsare-Tsare ta Kasa wacce take kula da Gidajen Zoo na Jamaika,” ta bayyana wa kafar labarai ta Our Today.
Ta ce wannan, ba shi ne zargi na farko ba game da kula da dabbobi a gidan Zoo na Jamaika. Ta ce,
“Wannan me yake nuna wa maziyarta gidan namun dajin? Me kuke yi yanzu idan yaro ya yi koyi da wannan mutum kuma ya ji mugun rauni ko ya mutu?”