Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwarta kan yadda masu safarar mutane ke ƙara amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yaudarar mutane da kuma yi musu cin zarafi, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana wadda ba ta da iyaka kuma mai saurin yaɗuwa wadda ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa.
Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na ƙasa karo na 27 kan safarar mutane da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba, Babbar Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi SAN, ya ce dole ne Najeriya ta ɗauki mataki ta hanyar zamani daidai yadda matsalar take saurin faɗaɗa.
Ministan shari’an ya ce, “Safarar mutane ta koma ta intanet. Dole ne mu gaggauta ɗaukar mataki ko kuma mu fuskanci barazanar wuce gona da iri daga masu aikata laifuka waɗanda yanzu suke amfani da manhajoji na zamani wajen samun waɗanda za su yi safara, juya su, da kuma yi musu cin zarafi ta intanet.”
Fagbemi ya bayyana safarar mutane a matsayin sana’ar laifi ta uku mafi samun riba a duniya, bayan safarar miyagun ƙwayoyi da fatauci makamai.
- NAJERIYA A YAU: Tasirin ’Yan Uwantaka Ga Rayuwar Al’umma
- ’Yan bindiga na neman N100m kafin sakin Faston da suka sace a Kaduna
Daga nan ya yi kira da a ƙara ƙarfin dokoki, hukumomi, da kuma hanyoyin fasahar zamani wajen magance matsalar.
Ya ce, “yaƙi da safarar mutane ba magana ce da ta tsaya kan bayar da alƙaluma ko wasu tsare-tsare ba, batu ne da ke buƙatar a yi a aikace domin tabbatar da adalci da ’yancin walwalar ɗan Adam da kuma kare martabar ƙasa.”
Don haka ya buƙaci kwamishinonin mata a duk jihohin Najeriya su yi ƙoƙarin damar da tsare-tsare da dokoki tare da kafa kwamitocin aiki da cikawa da kuma kasafi da za su taimaka kai-tsaye wajen yaƙar matsalar.
A nata ɓangaren, Babbar Daraktan Hukumar Hana Safarar Mutane ta Kasa (NAPTIP), Binta Adamu Bello, ta bayyana cewa hukumar ta riga ta fara ƙara ƙarfinta a fannin fasahar zamani.
Ta ce, “Yaƙinmu ya koma intanet, kuma martaninmu ma ya koma can,” inda ta bayyana cewa an horar da jami’an tattara bayanai sama da 160 a faɗin ƙasar, yayin da aka kuma ƙaddamar da sabbin manhajoji na zamani domin bibiyar batutuwan safarar ɗan Adam da kuma haɗin gwiwa.
Binta Bello ta ce hukumar ta ceto tare da gyara rayuwar sama da mutane 7,000 tsakanin shekarar 2022 zuwa 2024, kuma an samu nasarar hukunta mutane 205 a cikin wannan lokacin.
Kazalika ta ƙaddamar da jami’an da kai guda 205 domin yaƙi da safarar mutane da kuma cin zarafi a faɗin Najeriya.
Haka kuma ta ƙaddamar da sabbin manhajojin zamani domin inganta tsarin tattara bayanai da kai rahoton safarar ɗan Adam, da haɗin gwiwar Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da Muggan Ƙwayoyi da Laifuka (UNODC) da kuma gwamnatin ƙasar Switzerland.
Sauran sun haɗa da farfaɗo da shafin hukumar na kai rahoto da tattara bayanan cin zarafin jinsi, kafa cibiyar zamani a Katsina da kuma farfaɗo da cibiyarta ta zamani a Legas, da gudummawar hukumomin ƙasa da ƙasa irin su ƙungiyoyin ECOWAS, EU da kuma gwamnatin ƙasar Netherlands.
Wakilin UNODC a Najeriya, Cheikh Toure, ya yaba wa ƙoƙarin Najeriya wajen yaƙi da safarar ɗan Adam, inda ya jaddada cewa “manufa ba ta da wani amfani ba tare da aiki a matakin ƙasa ba.”
Ya buƙaci a ƙarfafa dokokin da kuma tsarin tattara bayanai da yanayin kula da waɗanda aka ceto, yana mai jaddada muhimmancin goyon bayan masu ruwa da tsaki a wannan gagarumin aiki.