Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta tsallaka zuwa wasan karshe na Gasar Zakarun Turai bayan da ta yi wa Real Madrid dukan kawo wuka da ci 4-0.
A wasanni biyu da suka buga, Real Madrid wadda sau 14 tana daga kofin, ta kwashi kashinta da jimillar ci 5-1 a hannun Manchester City.
Karo na biyu ke nan da Manchester City take kaiwa wasan karshe na Gasar Zakarun Turai a cikin shekaru uku, inda a wannan karon za ta fuskanci Inter Milan a a birnin Santanbul na kasar Turkiyya a ranar 10 ga watan Yuni, 2023.
Manchester City na fatan cika babban burin mai kungiyar, Sheikh Mansour, na daga kofin Gasar Zakarun Turai, tun bayan da ya sayi kulob din a shekarar 2008 — amma Chelsea ta rika shan gabansu a kakannin wasa biyu da suka gabata.
A wasan City da Madrid na daren Laraba a filin wasa na Etihad, yunkurin Madrid na daga kofin a karo na 15 ya fara gamuwa da tarnaki ne bayan da Bernardo Silva na Manchester City ya zura mata kwallaye biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Ana cikin haka kuma dan wasanta Eder Militao yi kuskuren zura mata na uku, kafin daga bisani Julian Alvarez ya cike na hudu.
A haka aka tafi hutun rabin lokaci tawagar Pep Guardiola na gaba da su da 4-0, kamar yadda Real Madrid ta yi musu a wasan kusa da na karshe a shekarar da ta gabata.
Kawo yanzu dai ba a doke Manchester City a gidanta a a wasanni 26 na Gasar Zakarun Turai.
Manchester City za ta kara da Inter Milan a matakin karshe inda take fatan cika babban burin mai kungiyar, Sheikh Mansour, na cin kofin Gasar Zakarun Turai, tun bayan da ya sayi kungiyar a shekarar 2008, amma Chelsea ta sha gabansu a kakannin wasa biyu da suka gabata.