✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zainab Suleiman Okino: Kyakkyawar misali ga matan Arewa

A tarihi, ita ce mace ta farko da ta taba zama Kwamishinar Yada Labarai a Kogi

Idan ana batu kan gogaggun matan da suka yi fice, har suka zama kallabi tsakanin rawuna a aikin jarida a Arewacin Najeriya, dole an ambaci sunan Zainab Suleiman Okino.

Ta shafe sama da shekara 30 tana gwagwarmaya a matsayin ’yar jarida, mai bincike, marubuciya, kwararriya a harkokin mulki kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum.

La’akari da tarin ayyuka da rubuce-rubucenta a jaridu da mujallu da shafukan intanet da kuma makalolin da ta gabatar a wurin taruka, ko shakka babu Tauraruwar tamu na daya daga cikin ’yan jarida mata mafi shahara a Arewacin Najeriya.

Wadannan da ma sauran dalilai ne suka sa Gwamnatin Tarayya, a yayin Babban Taron Kasa na shekarar 2014 ta zabo ta a matsayin daya daga cikin ’yan jaridar da aka sahalewa su dauko rahoton abin da ya wakana a wajen, inda irin rahotanninta a lokacin suka sa ta yi zarra a tsakanin takwarorinta.

Gwagwarmayarta a aikin jarida

Ta fara aiki a tsohon kamfanin jaridar Today da ke Kaduna a shekarar 1989 a matsayin wakiliya, har ta zama Editar Harkokin Mata, sannan ta koma mujallar Citizen, ita ma a Kaduna a matsayin Edita tsakanin 1991 zuwa 1994.

Ta koma kamfanin Media Trust, mawallafa jaridun Daily Trust da Aminiya a shekarar 1998 a matsayin Editar Tsare-tsare ta farko a bangaren jaridun karshen mako, kafin daga bisani ta zama Mataimakiyar Edita ta Daily Trust, har zuwa lokacin da ta zama Mataimakiyar Shugabar Hukumar Editoci ta kamfanin.

Gudunmawarta ta taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarorin da kamfanin ya samu, har ya zama daya daga cikin jaridun da karansu ya kai tsaiko a Najeriya.

Daga nan ne a shekarar 2009 ta koma kamfanin jaridar Leadership a matsayin Editar Gudanarwa, sannan ta yi aiki a kamfanin jaridar The Sun, nan ma a matsayin Edita

Zainab Okino ta kuma taba zama Shugabar Hukumar Editoci ta kamfanin jaridar Blueprint, sannan ta zama Babbar Edita, kuma ana ganin gudunmawarta a kamfanin ta taimaka matuka wajen shahararsa cikin kankanin lokaci.

Tauraruwar tamu dai ta yi karatun digirinta na farko ne a fannin Tarihi a Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) a shekarar 1987, kafin daga bisani a 2002 ta samu takardar shaidar digiri na biyu a fannin Harkokin Kasa da Kasa da Diflomasiyya (MIAD) daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU).

Kyaututtukan da ta taba samu

Kadan daga cikin jerin kyaututtukan da Hajiya Zainab Okino ta samu saboda gudunmawarta wajen ci gaban al’umma sun hada da ta zama dalibar wani shirin Gwamnatin Amurka kan alakar Gwamnati da kafafen yada labarai a jihohin Washington DC, Atlanta, Phoenix da San-Francisco a shekarar 2004 da kuma halartar wani taron kara wa juna sani ga mata Editoci a shekarar 2001 da dai sauransu.

Wadannan, da ma sauran abubuwa suka sa a ’yan shekarun baya aka nada ta mukamin Kwamishinar Yada Labarai ta Jihar Kogi tsakanin 2014 zuwa 2015, mace ta farko da ta taba rike matsayin a tarihin jihar.

Hajiya Zainab har ila yau mamba ce a kungiyoyin ’yan jarida da na jami’an hulda da jama’a da dama kamar su NIPR da NUJ da NAWOJ da kuma NGE.