✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zagon kasa: APC ta dakatar da Sanata mai ci da wasu mutum 56 a Gombe

Jam'iyyar ta zarge su da yi mata zagon kasa a zabukan da suka gabata

Jam’iyyar APC a Gundumar Bamban a Karamar Hukumar Balanga a Jihar Gombe, ta kafa kwamiti don bincikar Sanatan Gombe ta Kudu, Bulus K. Amos, bisa zargin yi mata zagon kasa.

Shugaban jam’iyyar a matakin gundumar Bamban, Muhammad Kaka, ya ce suna zargin Sanata Bulus da yi wa APC zagon kasa a zaben shugaban kasa da na gwamnoni.

Kaka, ya ce hakan yasa suka kafa kwamitin bincike don gano aikin da ya yi wa jam’iyyar adawa da ya sa har APC ta fadi a dukkan rumfunan zaben da ake da su a yankin.

Kazalika a gundumar Lubo da Difa da Kinafa da ke Karamar Hukumar Yamaltu-Deba, jam’iyyar ta gano cewa dan majalisar wakilai mai wakiltar Yamaltu Deba, Yunusa Ahmad Abubakar Ustaz da wasu mutum 56 sun yi wa jam’iyyar APC zangon kasa, wanda hakan ya sa aka dakatar da su.

Shugaban jam’iyyar APC a gundumar, Maina Amadu ne, ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata a garin Lubo.

Shugaban ya ce matakin ya biyo bayan tuntubar dukkanin shugabannin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki tun daga matakin gunduma zuwa karamar hukuma zuwa jiha sannan suka dakatar da su.

“Muna da hujjojin da muka tattara a kan wadanda aka dakatar a lokacin yakin neman zabe suna raba kudi ga masu zabe don su zabi ‘yan takarar wasu jam’iyyu a kowane mataki idan ban da Sanata Muhammadu Danjuma Goje.

Shugabannin biyu suka ce jam’iyyar za ta yi wa ’ya’yan da aka dakatar bayani a hukumance kan matakin da ta dauka, tare da basu damar kare kan su.