✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Shugaban Kasa: Atiku ya lashe Bayelsa

Atiku ya doke Peter Obi da Tinubu

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya lashe Jihar Bayelsa.

Atiku dai ya sami nasarar ce bayan ya doke Bola Tinubu na APC da kuma Peter Obi na LP.

Jami’in tattara sakamakon zabe a Jihar, kuma Shugaban Jami’ar Benin, Farfesa Lilian Salami ne ya sanar da sakamakon zaben a Yenagoa, babban birnin Jihar ranar Litinin.

Ya ce Atiku ya sami kuri’a 6,8818, yayin da Peter Obi na LP ya sami kuri’a 49,975.

Sakamakon ya kuma nuna Bola Ahmed Tinubu na APC ya sami kuri’a 42,572, inda ya zo na uku.