✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Sanatan Kogi: Smart Adeyemi ya kayar da Dino Melaye

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta tabbatar da Smart Adeyemi na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar Dan Majalisar…

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta tabbatar da Smart Adeyemi na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kogi ta yamma.

Yayin da yake bayyana sakamakon zaben a daren jiya Asabar, Baturen zaben, Farfesa Olajide Lawal, ya bayyana cewa Smart Adeyemi, na jam’iyyar APC ya samu kuri’u dubu 88,373, yayin da Dino Melaye na PDP ya samu kuri’u dubu 62,133.