✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Osun: Masu zanga-zanga sun taru a matattara sakamako

Masu zanga-zangar sun ce ba su yarda a yi "inconclusive" ba.

Rahotanni daga Osun sun ce wasu masu zanga-zanga sun yi wa ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke Osogbo, babban birnin Jihar, tsinke.

A ofishin na INEC ne dai ake tattara sakamakon kananan hukumomi; a can ne kuma za a sanar da wanda ya lashe zaben.

Hakan na faruwa a daidai lokacin da Babban Baturen Zabe na Jihar, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe, yake fara karbar kammalallaen sakamakon daga turawan zabe na kananan hukumomi.

Masu zanga-zangar dai sun ce sun taru ne don tabbatar da cewa ba a ayyana zaben a matsayin inconclusive (wato bai kammala) ba.

Sai dai wani jami’in INEC ya tabbatar da cewa zaben na Osun ba zai taba zama inconclusive ba domin tuni sakamakon kananan hukumomin jihar 30 ya isa hannun Hukumar.

Ko da yake an sanar da sakamakon zaben a wadansu kananan hukumomi, sai yanzu aka fara tattara su a matakin jiha.

Aminiya ta bayar da labarin cewa a Jihar ta Osun ne aka fara ayyana zabe da cewa bai kammala ba.

Jam’iyyu fiye da 10 ne dai suka yi takara, amma fafatawa ta fi zafi a tsakanin jam’iyyun APC da PDP.